Adamawa ta bi sahun Mayar da Almajirai Jihohinsu

Gwamnatin jihar Adamawa ta fara mayar da dalibai sama da 400 zuwa jihohin su na asali.

Sakataran Gwamnatin jihar Bashir Ahmad, ya bayyana haka a yayin da aka fara mayar da almajiran zuwa jihohin su, domin dakile yaduwar cutar corona a jihar.

An bayyana cewa yawancin daliban da aka maida zuwa asalin jihar su, sun fito ne daga jihar Gombe.

Haka kuma sakataran ya bayyana cewa mayar da daliban da Gwamnatin jihar Adamawa tayi, matsayace kan yarjejeniyar da kungiyar gwamnoninin arewa suka cimma.

Gwamnatin jihar tace gabanin mayar da almajiran zuwa jihohinsu na asali, wasu gwamnonin jihohin arewa, tuni suka dawo mata da wasu yara yan asalin jihar.

Adamawa StateAlmajiraialmajiriArewa
Comments (0)
Add Comment