Sakataran harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa kasar Japan domin halartar taro Ministocin kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 domin lalubo hanyoyin warware rikcin Gaza da kuma tsagaita wuta tsakanin dakarun Hamas da Isra’aila.
Mista Blinken kawo yanzu dai bai yi wani jawabi a taron na kwanaki uku da za’a ayi a Birnin Tokyo na kasar Jaban ba, dangane da rikicin da ya barke a gabas ta tsakiya.
A cewar hukumomin Israla’ila, kawo yanzu Isra’ila na cigaba da kai munanan hare-hare kan Gaza a matsayin ramuwar gayya tun bayan da Hamas ta kaiwa Isra’ila hari ranar 7 ga watan oktoba wanda ya kashe fiye da Isra’ilawa 1,400 galibi fararan hula.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas, adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarce mutane dubu 10, cikin su hadda kananan Yara 4,000.
Amurka dake a matsayin Babbar kawa ga Isra’ila tayi kira da tsagaita wuta a yakin da ake cigaba da gwabzawa.
Mista Blinken yace gwamnatin Washington na yin aiki tukuru domin kai agaji ga fararan hula.
Yayinda fadar gwamnatin White House tace shugaba Joe Biden da Firaminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu na tattaunawa domin kawo karshen yakin. Amma Mista Netanyahu yayi alkawarin shafe kungiyar Hamas a bayan kasa.