Mafi yawancin lokuta kasala kan zo mana, jiki yayi nauyi. A lokacin kishingida ko dan runtsawa shi ne abin da wasu kan son yi, yayinda wasu kuma kan bukaci samun dan abin tsotsawa ko kurba ko kuma taunawa.
Amma sai dai ba kowannenmu ba ne yake da masaniyar illoli da kuma alfanun yadda muke tafiyar da rayuwar ta yau da kullum ba, wanda hakan kan iya haifarwa jiki matsala cikin sauki ba tare da an lura ba.Lafiyarmu Jarinmu, don haka ne ya kamata muyi iyakar kokarinmu don kare kanmu.
Sauya yadda muke tafiyar da tsarin rayuwarmu zai iya taimakawa matuka cikin lokaci kadan.Don haka ne muka kawo abubuwa 3 da kwata-kwata bai kamata a aikata ba bayan cin abinci, amma a sani akwai karin abubuwan da basu da kyau bayan kamala cin abinci kuma likita zai fadawa duk mai son sani idan ya tambaya.
Yanzu ga uku daga ciki:
Bacci
Bacci bayan cin abinci na iya haifar da rashin jin dadin jiki, kunar zuciya da sauransu. Wani bincike da aka yi a jamiar Ioannina Medical School ya bayyana cewa mutanen da suke tsahirtawa kafin yin bacci bayan sun ci abinci, ba su fuskantar hadarin yanke jiki su fadi sosai idan aka kwatanta su da masu afkawa bacci da zarra sun gama kalaci.
Saboda haka ne ya cancantu a dan jira na wasu awanni kafin fadawa duniyar bacci.
Shan Taba
Shaye-shaye na matukar illata lafiya, haka zalika shan sigari bayan cin abinci na iya janyo matsaloli ga gangar jiki. Taba na kunshe da sinadaran da ke illata hanyoyin numfashi wanda kuma yana da alfanu sosai wajen narkar da abinci.
Shan karan Sigari guda bayan cin abinci daidai yake da shan kara 10 a lokaci guda a cewar masu ilimin kimiyya, kana hakan na iya kara hadarin kamuwa da cutar sankarar hunhu.idan har ya zama dole sai an sha sigarin, to lallai a tabbata sai bayan shafe akalla sama da mintuna 20 da cin abinci.
Wanka
Domin narkewar abincin da muka ci, ciki na bukatar bugawar jini sosai. Sai dai, yi wanka bayan cin abinci kan sauya akalar tafiyar jinin zuwa kafafuwa da hannaye, wanda hakan ke rage karfi wajen saurin narkar da abinci, watakil ma har ya janyo ciwon ciki.
Ana iya duba don samun wasu bayanan healthy-lifebox.com