A yau Laraba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke kaddamar da ranar dimokradiyya a karon farko, bayan mayar da ita zuwa bikin 12 ga watan Yuni maimakon 29 ga watan Mayu kamar yadda aka saba a baya.
Bikin ranar 12 ga watan Yuni, na tunawa ne da zaben shugaban Najeriya na 1993, wanda akasarin mutane suka yi imani cewa sanannen dan siyasar kasar marigayi Cif MKO Abiola ne ya yi nasarar ci, kafin gwamnatin mulkin soja ta lokacin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ta soke zaben.
Kafofin labaran Kasar nan sun ruwaito cewa, Shugaba kasa Buhari ya sanya hannu a kan kudurin dokar da ya mayar da 29 ga Mayu ranar mika mulki, ita kuma 12 ga Yuni ta kasance ranar hutu don bikin dimokradiyya a kasar.
Sai dai kuma a wani bangaren, wasu tsoffin ‘ya’yan tsohuwar jam’iyyar NRC a jamhuriya ta uku, sun kalubalanci matakin mayar da 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokradiyya’Ya’yan tsohuwar jam’iyyar NRC sun ce ba sa goyon bayan wannan mataki, don a cewarsu dan takararsu Alhaji Bashir Tofa ne ya ci zaben, amma ba Moshood Abiola na SDP ba.