Abu ne mai sauki idan aka ce daya a tara da daya kowa ya ce biyu, amma sai dai wani lokacin abin kan zamo a dukunkune. Batu zan yi na ainihin dalilin da ya sanya gwamnatin tarayya ta zabi ta sako jagoran mabiya shi’a Ibrahim Elzakzaky a yanzu duk kuwa da cewa an sha bayar da shi beli a baya amma tayi kunnen uwar shegu da umarnin kotun.
Tarihi – Yana da kyau kowa ya sani cewa ba wannan ba ne na farko da Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take yin biris da umarnin kotu, hakan ta faru akan tsohon mai bawa shugaban kasa shawara Kanal Sambo Dasuki mai ritaya.
Rashin Mafita – A daidai lokacin da yan shi’ar suka matsa kaimi da yin zanga-zanga, wanda har takan zamo sanadiyyar asarar dukiya da rayuka, sai ga wata fitinar daban ta bullo daga yankin yammacin kasar nan ta masu neman ayi juyin juya hali karkashin jagorancin Omoyele Sowore.
Neman Masalaha – Tuntuni ya kamata a ce an nemo hanyar magance matsalar kafin a fara rasa rayuka a hatsaniyar. Iya wadanda suka mutu a karon farkon rikicin Sojoji da yan shi’ar ya isa haka; amma kash har sai da ta kai cewa Wani matashi mai bautar kasa da kuma wani babban jami’in tsaro na yan sanda sun rasa ransa tare da wasu daga cikin mabiya shi’ar tukunna aka sake sabon lissafi.
Dalilin Sako Zakzaky
To yanzu dai a dalilin bullowar sabuwar fitinar masu neman kifar da gwamnati, ya zama dole ita gwamnati ta mayar da hankalinta waje guda domin fuskantar wannan sabuwar fitina kafin karamar Magana ta zama babba kuma dama ga shi akwai sauran kalubalen tsaro da kasar ke fama da su irinsu: Tsagerun Niger Delta, Boko Haram, Rikicin Makiyaya da Manoma da kuma Yan Bindiga masu garkuwa da mutane.
Saboda da haka gwamnati ba zata iya yarda ta karawa kanta wani nauyin matsalar tsaron ba don haka ne ta zabi ta magance ta yan Shi’a ta hanyar yi mata kwab daya sannan ta kuma murkushe masu neman ayi juyin juya halin.
Zamu iya cewa Gwamnatin ta kuwa cimma burinta domin ko ina ka duba Shewa akeyi a kafafen sada zumunta da kuma san barka domin sakin shugaban yan shi’ar.
Kana kuma a hannu guda jami’an tsaro suka tabbatar sun murkushe yan zanga-zangar juyin juya halin ta hanyar shaka musu hayaki mai sanya hawaye wanda dama can basu samu wani goyon bayan da yayi tasiri a yankin arewa ba.
Yanzu dai hankalin kowa zai koma ne kan magance matsalar tsaro ta tsagerun Niger Delta masu fasa bututun mai, Boko Haram, Rikicin Makiyaya da Manoma da kuma Yan Bindiga masu garkuwa da mutane.
Ai hakane da akai shine maslaha da zaman lafiyar qasarmu