Abba Gida-gida ya lashe lambar yabo ta gwamna mafi ƙwazo a Afirka

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kashe lambar yabo ta “Gwarzon Gwamna na Afirka na Shekara” a fannin kyakkyawan shugabanci a bikin bayar da lambobin yabo Karo 14 na mujallar African Leadership Magazine (ALM) da aka gudanar a Casablanca, Morocco.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin, ya fitar a madadin wasu masu taimaka wa shugabannin Afirka da suka halarci taron a Otal din Marriot, Casablanca.

Wannan girmamawa ta nuna irin nagartar shugabancin Gwamna Yusuf wajen inganta gaskiya, adalci da shugabanci na kowa da kowa, acewar sanarwar.

Acewar Sanusi, Bature, sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo a fannin ilimi, gine-gine, kiwon lafiya, da bunkasa tattalin arziki sun sanya Jihar Kano zama abin koyi wajen kyakkyawan shugabanci a Afirka.

Gwamnan ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin jiha, Alhaji Usman Bala, wanda tsohon shugaban ma’aikata ne. Gwamnan ya mika wannan lambar yabo ga al’ummar Kano, yana jaddada rawar da suka taka wajen cimma nasarorin da gwamnatin ke samu.

A cewar mujallar African Leadership Magazine, a karkashin jagorancin Gwamna Yusuf, Kano ta samu manyan nasarori ciki har da ware fiye da kashi 31% na kasafin kudin jihar ga fannin ilimi, tallafa wa dalibai masu karatun digiri na biyu a kasashen waje, da kuma amfani da fasahar zamani wajen gudanar da mulki.

Comments (0)
Add Comment