Aƙalla mutum biyu ne suka rasu bayan wata tankar gas, ta yi bindiga a gadar Obiri zuwa Ikwerre da ke Gabas maso Yammacin Fatakwal a Jihar Ribas.
Lamarin ya faru da ƙarfe 9:25 na safe, bayan tankar ta faɗi a lokacin da ta ke ƙoƙarin ƙetare gadar sama, inda ta yi karo da wata mota ɗauke da mutane biyu a ciki.
Gadar sama ta Obiri zuwa Ikwerre na kan hanyar zuwa filin jirgin saman na Fatakwal, a Omagwa a Ƙaramar Hukumar Ikwerre.