Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ce zai taimakawa kasashen Afirka da maganin rigakafin cutar korona miliyan 15 domin yiwa jama’a rigakafi.
Erdogan dake jawabi ga taron shugabannin nahiyar dake halartar taro a Santanbul, yace jinkirin da ake samu wajen yiwa jama’a rigakafin cutar a Afirka wata gazawa ce ga Bil Adama baki daya.
Turkiya ta zuba jari sosai wajen bunkasa kasuwanci da harkokin diflomasiya tsakanin ta da kasashen Afirka tun bayan hawa karagar mulkin shugaba Erdogan a shekarar 2003.
Rahotanni sun ce an samu karuwar masu harbuwa da cutar korona a nahiyar Afirka, inda a makon jiya kawai aka samu karin kashi 57.
Kasar Afirka ta Kudu ke sahun gaba wajen samun yawan masu harbuwa da cutar, yayin da ta zama kasa ta farko da aka gano sabon nau’in cutar da ake kira Omicron, wanda aka bayyana cewar yafi saurin yaduwa daga sauran nau’oin cutar da aka gani.
Erdogan ya bayyana cewar Turkiya na shirin karfafa danganta da kasashen Afirka ta fuskar kula da lafiya da tsaro da noma da makamashi da kuma fasaha.
Erdogan yace Turkiya na aikin samar da maganin cutar korona na kan ta da ake kira Turkovac wanda ake nazari akan sa domin amincewa da shi a matakin duniya.