Helkwatar tsaro tace sojin sama na opearation Hadarin Daji sun lalata karin wani sansanin barayi tare da kashe batagari da dama a dajin Kwayanbana a jihar Zamfara.
Jagoran yada labaran ayyukan tsaro, John Enenche, cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja yace anyi luguden wuta ranar 7 ga watan Yunin da muke ciki, a cigaba da yakin sama da ake gudanarwa karkashin shirin operation accord.
- Matsalar wuta na ƙara ƙamari a jihohin Kano da makwabta
- Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 5 a Jihar Gombe
- An ƙaddamar da shirin rigakafin cutar Polio a yankin tafkin Chadi
- Nan da wata 6 yankin Arewacin Najeriya zai fitar da matsayarsa kan zaben 2027 – Hakeem Baba Ahmad
- An soki yadda aka kafa Kwamatin Kidaya a Najeriya
Majon Janar Enenche yace an samu nasarar bayan wani rahoton sirri, leken asiri da sa’ido ya tabbatar da cewa an boye wasu tantuna a karkashin duhun bishiyoyin dajin.
Yace rahoton sirrin ya kuma bayyana cewa ana amfani da
kogo da ake samu a wajen a matsayin maboyar barayin tare da sanannen jagoransu,
Dogo Gede.