An Rage Kudin Aikin Hajji A Jigawa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta ce za ta karbi mafi karancin kudin aikin hajjin bana zuwa kasar Saudi Arabiya.

Mai Magana da yawun hukumar Alhaji Hashimu Kanya ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Dutse, inda ya ce gwamnatin jihar ta rage kudin aikin hajjin bana.

Ya ce sabon kudin aikin hajji  bana zai kasance Naira milyan 1,464,322.12kb, sabanin naira milyan daya da dubu dari shidda.

Kanya ya ce wadanda suka bada kudin babbar kujera za a dawo musu da naira 49,475,98kb.

Yayin da za a dawowa da wadanda suka biya kudin karamar kujera Naira 35,677.88kb

Kazalika ya ce wadanda suka bada kudin ajiya na naira milyan daya za su ciko naira 464,322.12kb

addiniJigawa
Comments (0)
Add Comment