Ƴan Nijar mazauna Libya sun buƙaci gwamnatin Nijar ta kai musu ɗauki

Ƴan Nijar mazauna Libya sun buƙaci gwamnatin Nijar ta kai musu ɗauki

Ƴan Nijar mazauna ƙasar Libiya sun koka kan mawuyacin halin da suke ciki a sakamakon wani gagarumin kamen ƴan Nijar da hukumomin ƙasar ta Libiya suka ƙaddamar kan ƴan Nijar.

Yanzu haka dai shaidu daga ƙasar ta Libiya sun bayyana cewa akwai ɗaruruwan ƴan Nijar da aka kama a kamen na bayan nan inda ake tsare da su a gidajen kurkuku dabam-dabam na ƙasar.

Ƴan Nijar ɗin na kokawa ne kan yadda kamen ya shafi hatta masu takardun zama da kuma yadda jami’an ke ƙwace masu dukiya da kwashe masu kadarori a wuraren zamansu.

Wasu daga cikin ƴan Nijar ɗin a ƙasar ta Libiya sun yi kira ga gwamnatin Tchiani da ta gaggauta saka bakinta a cikin lamarin domin ganin hukumomin ƙasar ta Libiya sun sako ƴan Nijar ɗin da aka kama a lokacin samamen wanda yanzu haka ake ci gaba da shi.

Comments (0)
Add Comment