Ƙungiyar Inter Miami ta lashe MLS Shield na ƙasar Amurka

Ƙungiyar Inter Miami na Amurka ta samu nasarar lashe kofin MLS Supporter Shied karon farko bayan ta doke ƙungiyar Columbus Crew da ci uku da biyu.

Fitaccen ɗan wasan Argentina, Lionel Messi ne ya zura ƙwallo biyu a wasan, sannan tsohon Luis Suarez ya zura ƙwallo na uku.

Shi dai wannan kofi na Shiled ana ba ƙungiyar da ta fi taka rawar gani a kakar ƙwallon ƙafar ƙasar ne, wanda ƙungiyar ta samu a sanadiyar nasarar da ta samu wasanta na jiya.

Wannan kofin shi ne kofi na 46 da Messi ya lashe, inda ya kafa tarihin zama ɗan ƙwallon da ya fi lashe kofuna a duniya.

“Mun samu nasarar wannan, sai kuma tunanin me za mu yi a gaba,” in ji Messi.

Inter Miami na buƙatar ƙarin maki biyu a sauran wasanni guda biyu da za ta fafata a gasar domin kafa sabon tarihin maki mafi yawa a gasar MLS, wanda ƙungiyar New England Revolution ta kafa da maki 73 a shekarar 2021.

Comments (0)
Add Comment