Ƙasashen Burkina Faso da Rasha za su rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta gina tashar makamashin nukiliya a yammacin Afirka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AIB ya bayyana.
Yarjejeniyar za ta kasance karshen tattaunawar da shugaban mulkin sojan Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traore ya yi da shugaban Rasha Vladimir Putin a watan Yuli, yayin taron Rasha da Afirka a Moscow.
Kafar yada labaran Rasha tace za a rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin Rosatom, hukumar makamashin nukiliya ta tarayya ta Rasha, da ma’aikatar makamashi ta Burkina Faso, a makon makamashi na Rasha na 2023.
A cewar hukumar makamashin nukiliya ta duniya, Al’ummar Burkina Faso kimanin kashi 20 cikin 100 ne ke samun wutar lantarki daya daga cikin mafi ƙarancin farashi a duniya Bayan da aka samu saɓani da galibin kawayenta na yammacin Turai, ciki har da Faransa da ta yi mulkin mallaka, Burkina Faso ta koma kasar Rasha domin samun tallafin tattalin arziki da na soji.