Ƙasar Ghana za ta ci gaba da rufe iyakokinta har sai abin da hali ya yi sakamakon guje wa ɓullar korona karo na huɗu.
Shugaban ƙasar ta Ghana Nana Akufo- Addo, shine ya bayyana hakan yayin wani jawabi inda ya ce gwamnatinsa tana sa ido kan irin barazanar da cutar ke yi da kuma yadda ake riga-kafin cutar a wasu ƙasashe kafin ta buɗe iyakokinta.
Tuni de mazauna wasu garuruwa da ke makwaftaka da kan iyakokin suka soma zanga-zanga sakamakon lokaci mai tsawo da aka ɗauka iyakokin a garƙame.
Manyan motocin kaya da ke kan hanya ne kaɗai aka amince ma wa su wuce.