Majalisar karamar hukumar Hadejia tace zata yi aiki kafa da kafa tare da sabbin kansiloli da aka rantsar domin cigaban karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar Alh Abdulkadir Umar Bala T.O ne ya sanar da hakan yayin rantsar da karin sabbin kansilolin guda 2 da kuma kansiloli masu gafa guda 2 da masu baiwa shugaban karamar hukumar shawara 2.