Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Arewa wato Arewa Consultative Forum (AC) ta ce ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta, Mamman Mike Osuman dangane da wasu kalamai da aka alaƙanta da shugaban a wani taronta da ta yi ranar Laraba a Kaduna.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta musanta wasu bayanai da ke yawo cewa, sun bayyana goyon bayan fito da ɗan takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Arewa a babban zaben 2027.
Sanarwar da ta fitar ta hannun Shugabanta da kuma Sakataren Cibiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu da Alhaji Murtala Aliyu Wazirin Dutse da kuma Matawallen Gombe, ta ce Mista Osuman ya yi wannan kalaman ne ba da yawunta ba.
Sanarwar ta ce Osuman ya yi furucin ne ba tare da tuntuɓa ko neman shawarwarin sauran jiga-jiganta ba, saboda haka ra’ayinsa ne ya faɗa amma ba da yawun kungiyar ba. Sai dai ƙungiyar ta kuma ce yankin na Arewa na fama da ƙangin talauci da matsalar tsaro da rashin ilimi, inda ta bayyana cewa gundarin matsalar yankin na hannun ‘yan Arewan.