A zaman da majalisar jihar Kaduna ta yi ranar Talata, ta umarci hukumar zabe ta gudanar da zabe a mazabar Sabon Garin Zaria, ta kori wakilin wannan gunduma a majalisar, wanda shine tsohon kakakin majalisar, Aminu Shagali.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa majalisar ta yanke wannan hukunci bayan Honarabul Shagali bai halarci zaman majalisar na kwanaki 120 ba kamar yadda yake a dokar kasa.
” A dalilin haka ina kira ga hukumar zabe ta gudanar da sabon zabe a mazabar Aminu Shagali saboda abinda ya yi saba wa doka ce.
Dan majalisan dake wakiltar Zariya da Kewaye, Ahmed Mohammed, ne ya jagoranci muhawara a kan wannan kudiri, kuma gaba dayan ‘yan majalisar sun amince da ayi hakan.
Wadanda aka dakatar har na tsawon shekara daya kuma sun hada da Mukhtar Isa-Hazo,tsohon mataimakin shugaban Majalisar jihar daga gundumar Basawa, Nuhu Goroh-Shadalafiya daga gundumar Kagarko, Yusuf Liman-Dahiru, gundumar Kakuri/Makera da Salisu Isa, gundumar Magajin Gari.
daya daga cikin laifin Aminu Shagali shine kin aikawa da wasikar neman gafara ‘yan majalisan bayan rikici da aki yi a majalisar wanda aka zarge shi da hannu a ciki dumu-dumu.
Tun bayan wannan rikici da aka yi aka dakatar da ‘yan majalisar da basu ga maciji da shugaban majalisar Yusuf Zailani wanda shine Kakakin Majalisar jihar.