Hukumar kula da harkokin ruwan sama ta kasa tace,ambaliyar ruwa da za’a fuskanta a Najeriya ba don an bude kogin Lagdo dake kasar Kamaru ba ne.
A cewar Darakta Janar na hukumar Clement Nze, yace za’a samu ambaliyar ruwan sakamakon rashin gina hanyoyin da ruwa zai bi,da rashin inganta magudan ruwa a fadin Najeriya.
Daraktan ya bayyana haka ne jiya a ofishin dake Abuja,yace koda dam din Lagdo ya rushe tasirin sa bazai wuce garin Numan na jihar Adamawa ba.
kazalika Darakta Janar na hukumar yana bayar da shawarar gina madatsun ruwa a dam din Neja da Benue da kuma hanzarta aiwatar da aikin gina madatsar ruwan Kashimbila a jihar Adamawa. Ya kuma bayyana cewa yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da Najeriya ta kulla a shekarar 2016 ba ta bukatar hukumomin Kamaru su sanar da Najeriya kafin fitar da ruwa daga madatsar ruwan Lagdo.