Al’ummar yankin Gaza na fama da matsananciyar yunwa sakamakon takunkumin shigar da kayan agaji da Isra’ila ta sanya musu
Yayin da hare-haren Isra’ila kan yankin Gaza na kasar Falasdinu ya raba mazauna yankin kusan milyan 2 da dubu 300 daga mahallansu, kididdiga ta nuna kaso daya bisa hudu na Al’ummar yankin na fama da matsananciyar yunwa sakamakon takunkumin shigar da kayan agaji da Isra’ila ta sanyawa Yankin.
Akallah mutum 88 ne suka mutu cikin wata sanarwar bayan kwana guda da ministan lafiya a Gaza ya fitar, sanadiyyar harin da Isra’ila ta kai, yayin da mutane 135 suka jikkata.
Sabbin hare-hare da Isra’ila ke kaiwa yankin Gazza, ya sanya adadin wadanda suka mutu a yakin zuwa dubu 31 da 272, tare kuma da raunata fiye da mutum dubu 73, da 24 tun bayan fara yakin a watan 0ctobar bara.
Tuni dai Ministan harkokin kasashen wajen kungiyar tarayyar Turai ta EU Josep Borrell ya jawo hankalin taron kwamatin koli na majalissar tsaron Amurka cewa Isra’ila na amfani da makaman yunwa a yakin da take a Zirin Gaza wajen azabtar da mutanen yankin.
Ya ce “ halin matsi da ake ciki a Gaza lamari ne da aka kirkireshi da gangan, inda ya buga misalin garkame iyakoki da hanyoyin shigo da kayayyakin agaji da suka hada da abinci da magunguna zuwa yankin da yaki ya daidaita.
Borrell ya kuma jinjina girman kalubalen da ake fama da shi a yankin na Gazza cewa “ya fi karfin ibtila’in girgizar kasa, ko Ambaliya, annoba ce da aka kakabawa yankin da ya zama wajibi kasashen Duniya su fito su yi Allah wadai da shi.