Al’ummar Indiya sun fara kaɗa kuri’a a zaɓen da aka kasa gida bakwai cikin makonni shida, inda kusan mutane biliyan ɗaya suka cancanci kaɗa ƙuri’a.
Jam’iyyar BJP mai mulki ƙarƙashin jagorancin Firaiminista Narendra Modi, ta kasance a kan karagar mulki tun shekara ta 2014. A yanzu kuma tana neman ƙarin wa’adi.
Yayin yaƙin neman zaɓe BJP na mayar da hankali kan ƙidar kishin addinin Hindu da ci gaban tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al’umma. Ita kuwa babbar abokiyar hamayyarta Jam’iyyar Congress ta ƙulla ƙawance da ɗimbin jam’iyyun siyasar yankin don ƙoƙarin daƙile farin jinin Mista Modi.