Al’ummar da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Maiduguri sun yi zanga-zanga kan rashin abinci

0 121

Daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Maiduguri, Jihar Borno, sun yi zanga-zanga kan rashin abinci da kayan tallafi bayan ambaliyar da ta auku ranar 9 ga Satumba, 2024.

Ambaliyar ta raba sama da mutane miliyan ɗaya da gidajensu tare da lalata muhimman gine-gine, inda da dama suka rasa damar samun abubuwan gudanar da rayuwa.

Masu zanga-zangar, yawancinsu daga unguwar Baga  suke Road, sun toshe hanyoyi don nuna fushinsu game da rashin kulawa da samun tallafin.

Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Borno, CP Mohammed Lawal Yusufu, ya yi kira ga mutanen da su kwantar da hankalinsu, yana tabbatar musu da cewa gwamnatin Jihar Borno tare da hukumomin NEMA da SEMA sun kaddamar da shirye-shiryen raba kayan tallafin da aka samu.

Ya kuma gargade su da su kauce wa toshe hanyoyi domin kada a sami cikas wajen isar musu da tallafin.

Gwamnatin Jihar Borno da kungiyoyin agaji suna aiki tare don samar da abinci, muhalli, da ruwan sha mai tsafta, yayin da ake ci gaba da kokarin kwashe mutum 50,000 zuwa wuraren zama na wucin gadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: