Al’umma a Minna sun gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa

0 213

Al’umma a Minna, babban birnin jihar Neja sun gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa, inda suka rufe manyan titunan da ke birnin.

Masu zanga-zangar sun hada da mata da matasa inda suke rera wakoki yayin da jami’an tsaro har da yan sanda ke gefe suna kallo.

Wasu mazauna birnin da suka tattauna da manema labarai sun ce tsadar kayan masarufi da rashin tabuka abin a zo a gani daga bangaren gwamnati wajen samar da sauki a lamarin ne ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.

Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba a lokacin da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi, ya ce gwamnati tana sane da irin kunci da wahalar da jama’a suke fuskanta a yanzu.

Ya ce gwamnati tana aiki domin rage halin matsi da aka shiga da kuma tasirin da ake gani sanadin cire tallafin mai. Sai dai jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyun adawa da ingiza masu zanga-zangar, domin bayyana cewa gwamnatin shugaba Tinubu ta gaza tafiyar mulki. Kamar yadda sakataren yada labaran jam’iyar FELIX MORKA YA BAYYANA.

Leave a Reply

%d bloggers like this: