Al’umma a kasar Indiya suna zanga-zanga kan hare-hare da ‘yan tawaye ke kai musu

0 204

Dubban masu zanga-zanga sun fantsama kan tittunan jihar Manipur da ke arewa maso gabashin Indiya.

Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki ‘yan tawaye na kai musu hare-haren bam da rokoki.

Ɗalibai sanye da kayan makaranta da ƙungiyoyin mata da sauran al’umma sun fito kwai da ƙwarƙwatansu ɗauke da alluna da tutoci suna alla-wadai da waɗannan hare-hare da sukayi sanadin mutuwar mutane akalla uku a ƙasa da mako guda.

Ko a jiya Juma’a sai da aka kashe wani malamin addini, bayan harba makamin roka kan rufin gidansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: