Allah ya yiwa matar shugaban darikar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi

0 460

Allah ya yiwa Matar Shugaban Darikar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Hajiya Zainab Dahiru Bauchi rasuwar a jiya Lahadi.

Manema Labarai sun rawaito cewa Marigayiyar ta rasu ne a lokacin da Mijin nata Sheikh Dahiru Usman Bauchi yake kasar Saudi Arabia domin yin Umrah, kuma tuni aka binne ta da misalin karfe 2 na Rana.

Marigayiyar ta rasu tana da shekaru 60 a Duniya, kuma tana da Yaya 3 a Duniya.

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana mutuwar Marigayiyar a matsayin babban rashi, ba ga Mijin nata shi kadai ba, harma ga Kasa baki daya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci Jami’an gwamnatin zuwa Gidan Malamin domin yi masa ta’aziyar rasuwar Matarsa a Bauchin, tare da rokon Allah ya bawa Iyalanta hakurin jure rashin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: