Alhazan Najeriya Na Fuskantar Barazanar Wata Cuta A Saudiyya

0 255

Hukumar alhazai ta Kasa ta aika ga sakon gargadi ga alhazan Najeriya akan yaduwar kwayar cutar Korona da kuma wata cutar numfashi mai hadari a Gabas ta Tsakiya da ake kira da Middle East Respiratory Syndrome.

An aika da sakon gargadin cikin wata sanarwa da shugabar sashen yada labarai ta hukumar alhazan, Fatima Usara, ta fitar a Abuja.

Fatima Usara tace kwayoyin cutar da ke yawo a iska, basu da tsayayyen rigakafi ko maganin ciwon.

A saboda haka, Hukumar take gargadi ga mahajjatan da kada su ci naman rakumin da bai gama dafuwa ba, ko shan nonon da ba a sarrafa an dafa ba.

Daga nan sai tace hukumar ta shawarci alhazan da suyi amfani da dabaru nasu na kansu damin kare kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: