Hukumar hasashen yanayi ta kasa Nimet, tace akwai yuyuwar samun mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohi 25 na kasar nan, nan da kwanaki 3 masu zuwa.
Hukumar tayi hasashen samun ruwan sama mai karfin gaske a wasu yankuna na jihohin Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Bauchi, Adamawa, Taraba, Benue, Niger, Kogi, Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Imo, Akwa Ibom, Abia, Ebonyi and Cross River State.
Kazalika hukumar hasashen yanayi ta kasa tace akwai yuyuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Legas,Ogun da kuma Adamawa.
Hukumar tayi hasashen samun ambaliya sakamakon mamakon ruwan saman a ranakun Alhamis da lahadi.
Kazalika, an shawarci jama’a da kada suyi tuku yayinda dake ruwan. Hukumar ta shawarci jama’a da su sanya ido don samun karin bayanai.