Akwai yiwuwar ambaliyar ruwa a kogin Neja da Benue

0 175

Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a jiya Juma’a ya yi gargadi kan yiwuwar ambaliyar ruwa a kogin Neja da Benue.

A wani taron manema labarai da ministan ya yi a Abuja, ya ce ruwa mai yawa na kwarara ta wadannan kogunan zuwa yankin Neja Delta.

Ya kuma yi kira da ayi taka tsan-tsan ta kowane fanni da kuma daukar matakan da suka dace don tunkarar duk wata matsalar ambaliya a yankin kudancin kasar nan.

Ya kuma jaddada bukatar shirye-shiryen magance matsalar ambaliya a yankin kudancin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: