Akwai yiwuwa a tilastawa ASUU shiga yajin aikin gama gari a fadin kasar nan

0 344

Mambobin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU), sun ce mai yiwuwa a tilasta musu shiga yajin aikin gama gari a fadin kasar nan, saboda abin da suka bayyana a matsayin rashin gamsuwa da yadda jihohi da gwamnatin tarayya ke tafiyar da bukatunsu.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu, ta ce an cimma matsayar ne bayan wani taron majalisar zartarwa ta kasa.

A cewarsa, ya zuwa yanzu, babu wani yunkuri da gwamnatocin suka yi don magance bukatunsu cikin shekaru goman da suka gabata.

Wasu daga cikin bukatu da ya lissafo sun hada da, sake duba yarjejeniyar gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU a shekarar 2009, da farfado da jami’o’in gwamnati, da biyan duk wani alawus alawus na ilimi, da suka hada da albashin da aka hana, da kuma basussukan karin girma.

Ya kara da cewa kungiyar za ta koma zama bayan makonni biyu, daga ranar Asabar, domin duba yadda lamarin yake tare da daukar kwakkwaran mataki na magance matsalolin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: