Akwai Gudummawar da ƙere-ƙere da Fasahar Sadarwa Zasu Bayar Wajen Yaƙi Da Korona – NITDA

0 382

Hukumar cigaban fasahar bayanai ta kasa NITDA, tayi kira da ayi amfani da kere keren fasahar zamani,  wajen magance kalubale da cutar Corona ta haifar.

Hukumar tayi kiran ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar, na tsokaci kan ranar kere kere ta duniya, da akayi a jiya talata.

Majalisar dinkin duniya dai ta sanya ranar 21 ga watan Afrilun kowacce shekara, domin tunawa da irin gudun mawa da kere kere zamani ya bayar, wajen saukaka rayuwa, dama magance matsaloli.

Haka kuma akan gudanar da bikin ranar domin yiwa masu ruwa da tsaki kaimi, wajen inganta fasahar kere keren, domin amfanarsa wajen shawo kan matsalar tattalin arziki, da na zamantakewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: