Akalla mutum 60 ne suka mutu yayin ambaliayar ruwan sama kamar da bakin kwarya a Afghanistan

0 159

Hukumomin Taliban sun ce akalla mutum 60 ne suka mutu a wata ambaliayr da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar a arewacin lardin Baghlan kuma Sama da mutum 100 kuma sun jikkata.

Kakakin ministan cikin gida ya shaida wa manema labarai cewa karin mutane masu yawa sun makale a cikin gidajensu.

Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwan da ke hankoro ya rika shafe gidaje a kauyuka da dama, ya bar wurare da dama a rushe.

Jami’ai sun ce an yi hasashen samun tsawa a cikin kwanaki masu zuwa wanda hakan zai iya kara adadin mutanen da abin ya shafa.

A yammacin Afghanistan a watan jiya, gwamman mutane ne suka rasa rayukansu a wata ambaliya da aka samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: