Akalla mutane takwas aka kashe a garin Yelewta na karamar hukumar Guma ta jihar Benue
Akalla mutane takwas aka kashe a garin Yelewta na karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce kisan ya faru ne lokacin da ‘yan kasuwa ke tashi daga shago.
Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, ya shaidawa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an yi wa wadanda abin ya rutsa da su kisan gilla.
Caleb Aba ya ce ranar kasuwar Yelewta ce kuma ‘yan kasuwa na shirin tashi, maharan dauke da makamai suka afka musu, inda suka kashe mutane takwas nan take.
Shugaban ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata asibiti domin samun kulawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane shida.