Akalla mutane 79 ne suka mutu sannan aka ceto sama da 100 bayan da jirgin ruwa ya kife a gabar tekun kudancin kasar Girka
Akalla mutane 79 ne suka mutu sannan aka ceto sama da 100 bayan da jirgin ruwa na kamun kifi da suke ciki ya kife a gabar tekun kudancin kasar Girka.
Sai dai wadanda suka tsira da ransu da jami’an kasar Girka sun ce akwai karin daruruwan bakin haure a cikin jirgin ruwan.
Gwamnati ta ce wannan na daya daga cikin manyan bala’o’in da suka shafi ‘yan ci-rani a Girka, kuma ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki.
Jirgin ruwan ya nutse ne a waje mai nisan kilomita 80 kudu maso yammacin birnin Pylos.
Jami’an tsaron gabar ruwan sun ce an ga jirgin ruwan a cikin ruwan kasa da kasa da yammacin jiya Talata, inda suka kara da cewa babu wanda ke cikin jirgin ruwan da ke sanye da rigar ruwa.
Jim kadan bayan haka, kwale-kwalen ya kife, inda ya dauki mintuna goma zuwa goma sha biyar kafin ya nutse gaba daya. An fara gudanar da aikin bincike da ceto amma guguwa mai karfi ta kawo tsaiko. Ana kyautata zaton jirgin ruwan ya taso ne daga kasar Libya zuwa kasar Italiya.