Akalla mutane 49 ne suka mutu biyo bayan ambaliyar ruwan sama a Arewacin Najeriya

0 148

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta ce akalla mutane 49 ne suka mutu, sannan dubbai suka rabu da muhallansu bayan mamakon ruwan sama da ya jawo ambaliya a Arewa Maso Gabashin Kasar na, kamar yadda Hukumar ta bayyana jiya Litinin.

Jihohin Arewa guda uku da suka fi fuskantar ambaliyar su ne Jigawa,Adamawa da  kuma jihar Taraba, kamar yadda Kakakin NEMA Manzo Ezekiel ya shaida.

A shekarar 2022, ansamu ambaliya mafi muni a cikin shekakarun da suka gabata, inda mutane 600 suka mutu, sannan kusan mutane miliyan 1.4 ne suka rasa muhallansu, sannan aƙalla hekta 600 na gonakine ya lalace.

Idan ba a manta ba, tun a farkon daminar bana Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa jihohi 31 daga cikin 36 ne suke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: