Akalla mutane 4,500 an kuma yi garkuwa da mutane 7,000 a karkashin mulkin Bola Tinubu

0 249

Wani bincike da kafafen yada labarai da kungiyoyi suka gudanar ya nuna cewa ayyukan ta’addanci sun hallaka akalla mutane dubu 4,500 yayin da aka yi garkuwa da mutane dubu 7 cikin shekara guda a karkashin mulkin Bola Ahmad Tinubu.

Yayin jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun bara lokacin da aka rantsar da shi, shugaban kasar ya sha alwashin tunkarar matsalolin ta’addanci da kuma rashin tsaro gadan-gadan.

Wannan ba shi ne karon farko da shugaban ke yiwa ‘yan Najeriya alkawarin magance matsalar tsaro ba, don kuwa ya kasance cikin manyan batutuwan da yake nanatawa a wajen yakin neman zabe.

To sai dai, shekara guda bayan darewarsa karagar mulki, a iya cewa babu wani sauyi na azo a gani a bangaren tsaro, illa ma dai sake sabon salon kai hare-hare da ‘yan bindiga keyi musamman a arewacin kasar nan, yayinda kungiyar Boko Haram tsagin Ansaru ke ci gaba da samun karfi.

Cikin makon da ya gabata kungiyar ta yi garkuwa da mutane 160 a jihar Neja, a wani hari da ba’a taba ganin irinsa ba a jihar.

Kungiyar ACLED mai tattara kididdigar kisa ko kuma mutanen da aka yi garkuwa da su ta ce bayananta sun nuna cewa mutane dubu 4,556 ne suka rasa rayukansu sannan  aka yi garkuwa da dubu 7,086 a tsakanin ranakun 29 ga watan Mayun bara zuwa 11 ga watan Mayun da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: