Akalla mutane 40 ne suka mutu a wani harin atilari kan wata kasuwa a Sudan

0 127

Adadin waɗanda suka mutu a wani harin atilari kan wata kasuwa a garin Sennar na Sudan, ya kai mutane 40, a daidai lokacin da ake fargabar alkaluman za su iya ƙaruwa.

Ana dai zargin dakarun RSF da kai harin a garin da ke kudu maso gabashin ƙasar, kamar yadda jaridar Sudan Tribune ta ruwaito.

Wata ƙungiyar likitoci ta bayyana a ranar Lahadi cewa dakarun na RSF sun kashe fararen hula 21 da kuma jikkata wasu 70 bayan ruwan bama-bamai da ta yi a kasuwar mai cike da cunkoso.

Harin ya zo ne jim kaɗan bayan da sojojin ƙasar suka kai hare-hare ta sama kan wuraren RSF a kudanci da kuma yammacin garin Sennar da kuma kusa da birnin Al-Suki.

Lauyoyi da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan’adam, sun kwatanta farmakin a matsayin saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, inda suka yi kiran gudanar da bincike mai zaman kansa.

A watannin baya-bayan nan, dakarun RSF sun tsananta kai harin makaman atilari kan yankunan fararen hula a kuma biranen da sojojin gwamnati ke iko da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: