Akalla mutane 37 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a Najeriya

0 117

Akalla mutane 37 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a halin yanzu, wadda ta ayanzu haka ta shiga jihohi 30 ciki har da Legas da Ogun.

Mataimakiya ta musamman ga gwamnan jihar Legas kan harkokin kiwon lafiya, Dr Kemi Ogunyemi, a cikin wata sanarwa jiya ta hannun daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Tunbosun Ogunbanwo, ta ce jihar ta samu karin mutuwar mutane 6 bayan fiye da mutum 15 da aka samu a baya.

Ta ce rahoton cutar ta kwalara ya kai 401 a jihar.

A nata bangaren, kwamishiniyar lafiya ta jihar Ogun, Dokta Tomi Coker, ta shaida wa manema labarai cewa jihar ta samu Karin mutuwar mutum daya baya ga mutum 14.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya, a rahotonta na baya-bayan nan, ta ce daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Yuni, 2024, sama da mutane 1,141 da ake zargin sun kamu da cutar, sannan sama da 65 ne aka tabbatar sun kamu da cutar ta kwalara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da 30, inda aka samu rahotannin cutar daga kananan hukumomi 96 a Jihohi 30.

Leave a Reply

%d bloggers like this: