Akalla mutane 32 aka kashe yayin farmakin da ‘yan bindiga suka kai yankin Abyei na kasar Sudan

0 248

Hukumomin  a Sudan a yankin Abyei dake takaddama a kai, sun ce akalla mutane 32 ne aka kashe bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyukan yankin.

Ministan yada labarai na Abyei, Bolis Kuoch, ya ce fiye da mutane 20 sun samu raunuka lokacin da wasu mutane suka bude wuta a safiyar jiya  Lahadi.

Ya ce dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun shiga tsakani don dakatar da tashin hankalin amma an kashe daya daga cikin sojojin.

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula tsakanin al’ummomin Abyei kan filaye.

Yankin da ke da arzikin man fetur, yana kan iyakar Sudan da Sudan ta Kudu, kuma ana ganin wani bangare ne na kasashen biyu, tun bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 2005. A makon da ya gabata ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kara wa’adin aikin wanzar da zaman lafiya na karin shekara guda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: