Akalla mutane 3 ne suka mutu hadarin mota da ya faru a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa

0 240

Akalla mutane 3 ne suka mutu biyo bayan wani harin mota da ya faru a karamar hukumar Taura ta nan Jihar Jigawa.

Wani Shaidar gani da Ido ya fadawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wata Mota tabi ta kan wani Dan Achaba da Fasinjojinsa biyu, a lokacin da yake kokarin tsallaka Kwalta a garin Kwalam.

A cewarsa, Mutane 3 da lamarin ya faru da sun mutu a nan take.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da hakan ga Manema Labarai.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce lamarin ya faru ne a jiya da daddare lokacin da wata Mota kirar Opel wacce ta fito daga karamar hukumar Taura domin tafiya Gujungu ta bige wani Dan Achaba wanda yake kokarin tsallaka Kwalta a garin Kwalam.

Jami’in Hulda da Jama’ar ya ce bayan faruwar lamarin Dan Achabar da Fasinjojinsa 2 sun mutu nan take.

Kazalika, ya ce tuni aka kai gawarwakin mutanen zuwa babban Asibitin Kwantarwa na Gagarawa, inda aka tabbatar da mutuwarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: