Kakakin hakumar yan sanda na jiha, DSP Lawan Shiisu Adam a cikin wata sanarwa daya fitar jiya ya tabbata da aukuwar hatsarin.
A mabanbancin lamarin kuma, zargin satar shanu ya tahar da hatsaniya a kauyen Maikambu da Balalashe dake karamare hakumar Garki, abinda yayi sanadin kona gidaje 5 zuwa 5 tare da jikkata mutane 6.
Yan sanda sun kama mutane 2 bisa hannu a zargin tayar da hargitsin, yayin da suke kokarin dawo da doka da oda a yankunan.
Haka kuma rundunar yansandan jihar jigawa tayi kira ga dukkan masu shirin shiga zanga-zanga daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta zuwa su gabatar da kansu ga rundunar.