Akalla mutane 2,000 ne suka amfana tallafin Shinkafa daga AA Rano a karamar Hakumar Hadejia

0 137

Akalla mutane dubu 2 ne suka amfana tallafin na buhunan Shinkafa mai nauyin kilo 25 a karamar Hakumar Hadejia da kewaye. Wanda gidauniyar AA Rano karkashin jagorancin shugaban rukinin kamfanin AA Rano Nig Ltd ke daukar nauyi a kowace shekara.

Wadanda suka amfana da tallafin sun bayyana jindadi da godiya ga attajirin, yayin da suke cewa tallafin yazo a daidai lokacin da ake bukatarsa.

Alhaji Umar Idris Kaka shine wakilin AA Rano a Hadejia yace wannan shine kashi na biyu a cigaban da rabon tallafin a wannan wata na Ramadana, sannan ya godewa Alhaji Auwal Abdullahi Rano bisa samar da tallafin ga alummar Hadejia kamar kowane lokaci.

Yace wadanda suka ci gajiyar tallafin a bana sun fito ne daga dukkan lungu da sakon Hadejia, ta hannu masu unguwanni da wadanda tan kwamatin rabon tallafin suka tantance.

Wannan dai ba shine karon farko da AA Ranon ke rabon tallafin a lokacin ibadar azumin Ramadan, lokacin bukukuwan Sallah, ko ibtilain ambaliyar Ruwa a Hadejia ba.

Leave a Reply