Akalla mutane 176 suka mutu sanadiyyar fari da tsananin yunwa

0 283

Akalla mutane 176 suka mutu sanadiyyar fari da tsananin yunwa a Yankin Tigray na kasar Habasha.

Wani babban jami’I a yankin Hadush Asemelash, ya fadawa gidan Talabijin na Tigray TV cewa wadanda suka mutu sun hada da maza 101 da kuma mata 75.

Gwamnan Yankin, yace akalla mutane dubu 45 a gundumar Emba Sieneti ke fama da matsananciyar yunwa tun bayan da aka fara yakin basarar kasar shekaru 2 da suka gabata.

Hukumomi a kasar sunce adadin wadanda ke barin gidajen su sakamakon fari da rashin kayan agaji na karuwa sosai.

A makon da ya gabata, gwamnatin Yankin Tigray ta sanya dokar ta baci bayan da mutane sama da 200 suka mutu sanadiyyar yunwa da fari.

Tunda da farko Majalisar dinkin duniya ta dakatar da kai kayan agaji yankin bisa zargin sata da ake tafkawa, lamarin da ya tsananta matsalar baga agaji.

Yankin Tigray na farfadowa daga yakin basasa shekaru 2 wanda ya kare a shekarar data gabata,

Leave a Reply

%d bloggers like this: