Akalla mata masu girka abinci 550 aka dauka a shirin ciyar da daliban firamare a karamar hukumar Hadejia
Akalla mata masu girka abinci 550 aka dauka a shirin ciyar da daliban firamare a karamar hukumar Hadejia.
Jami’in kula da shirin na karamar hukumar, Alhaji Musa Ibrahim Baderi ya sanar da hakan ga jami’in yada labarai na karamar hukumar Hadejia Muhammad Garba Talaki, bayan da aka raba kudade ga masu girka abincin na wannan watan na Augusta.
Ya ce a kowane wata, ana biyan kudi naira miliyan 24 da dubu 386 da 600 ga masu dafa abinci a yankin, ta hannun ma’aikatar agaji ta tarayya.
Jami’in kula da shirin ya ce makarantun firamare 56 ne ke cin gajiyar shirin a fadin karamar hukumar.
Ya shawarci masu dafa abinci da su kiyaye dukkan ka’idojin da aka tsarawa shirin domin dorewarsa.
Musa Baderi ya kuma hori masu dafa abincin da suke dafa abinci mai tsafta domin daliban.