Akalla likitoci 16,000 ne suka fice daga Najeriya cikin shekara 6 – Pate

0 80

Likitoci 16,000 sun fice daga Najeriya cikin shekara biyar ko shida, in ji Ministan Lafiya Muhammad Pate.

Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito ministan na magana yayin wani taron ƙara wa juna sani na ƙungiyar likitoci ta Association of Medical Councils of Africa (AMCOA) ranar Talata, yana mai cewa hakan ya jawo wa ƙasar asarar biliyoyin naira.

Ya ce ƙiyasin kuɗin da ake kashewa wajen bai wa likita ɗaya horo a Najeriya ya zarta dala 21,000, inda ya nuna damuwa game da yadda Najeriya ke asarar irin waɗannan kuɗaɗe.

“Wannan lamari ba wai magana ce kawai ta mutanen da ke ficewa ba, hakan na nufin asara,” in ji ministan.

“Yana shafar ɓangaren kula da lafiyarmu sosai, inda yankunan ƙauyukanmu suka fi shiga haɗari.”

Ya ƙara da cewa yanzu yawan mutanen da likita ɗaya ke gani a Najeriya ya ƙaru zuwa miliyan 3.9, wanda ya zarta adadin da hukumar lafiya ta duniya ta ƙiyasta sosai.

Leave a Reply