Akalla kimanin jarirai 10 ne ake binnewa a kullum a babbar makabartar Gombe, wacca ke da nisan kilomita 3 daga babban birnin na Gombe.
Ma,aikatan dake kula da wannan makabartar ne suka bayyana hakan a lokacin da suke tattauanwa da gidan jarida na Dailytrust, inda suka kara da cewa cikin watanni uku da suka gabata akalla an binne kimnanin mutane 750, baya ga jaririn da ake binnewa a kullum da suka kai mutum 10.
Adadin jaririn sunhada da wadanda ake yin barin su, da kuma wadanda suke mutuwa kafin a radamusu suna.
Inda suka kara da cewa basu da adadin yawan jaririn da ake binnewa a kullum a makabartar amma akalla a kullum ana binne akalla kimanin 10.
Babban jami’in dake kula da makabartar Muhammadu Tasha mai shekaru 57 ya tabbatarwa manema labarai wannan adadin.
Inda yace yana fara aiki a makabartar tindaga karfe 7 na safe zuwa 8 na dare, wanda yake hanashi yin wasu ayyukan rayuwarsa wadanda suka hada rashin halartar daurin aure, Suna, dadai sauransu.