Akalla fasinjoji 12 ne suka rasa rayukansu a babbar hanyar kaduna zuwa Abuja a wani mummunan hadari

0 277

Akalla fasinjoji 12 ne suka rasa rayukansu a jiya litinin a babbar hanyar kaduna zuwa Abuja, bayan motar da suke ciki tayi mummunan hadari.

Yayinda  mutane 6 suka jikkata, wanda kuma su ke karbar magani a asibiti.

Kwamishin tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Auwan shine ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace motar da tayi hatsarin  kirar Toyota Hiace wanda take dauke da mutane 18.

Samuel Aruwan yace lamarin ya faru ne a Nasarawa Doka dake yankin Kachia a jihar ta Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa akan lamarin, cikin wata takardar ta’aziyya da aka aikewa yan uwa wadanda suka rasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: