Akalla fararan hula 10 aka kashe yayin musayar wuta tsakanin RSF da sojojin Sudan
Akalla fararan hula 10 aka kashe bayan dakarun kai daukin gaggawa na RSF da sojojin Sudan sunyi musayar wuta a kudancin babban Birnin kasar Khartoum.
Fararen hula dama ne suka mutu a Sudan tun bayan fara yaki a watan Afrilu shekarar 2023 tsakanin dakarun RSF masu sanye da kayan sarki da sojojin kasar.
Fada ya tsananta tsakanin bangarorin 2 cikin makon da ya gabata, inda ya fantsama zuwa biranen Omdurman da Bahri masu makwabtaka lamarin da yayi sanadiyyar rasuwar dubban sojoji.
A cewar majalisar dinkin duniya, rikicin yayi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 12 da kuma raba mutane milyan 7 da muhallan su.