Bayanai daga Burkina Faso na cewa akalla fararen hula 44 sun mutu, a sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai kan kauyukan Kourakou da Tondobi da ke gab da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar, kamar yadda gwamnan yankin ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa.
Rahotanni sun ce ‘yan ta’adda sun kai hari kauyukan ne a tsakar daren ranar Juma’a, inda kuma suka bude wuta kan mai uwa da wabi lamarin da ya hallaka mutane 44.
A Karin bayanin da ya yi, gwamnan lardin Rodolph Sorgho ya ce mutane 31 ne aka kashe a kauyen Kourakou sai wasu 13 da suka mutu a kauyen Todobi.
Rabon da yankin ya ga irin wannan mummunan harin tun wanda aka kai a watan Yulin bara, wanda ya lakume da rayukan mutane 86.
Burkina faso daya daga cikin matalautan kasashen duniya ta shiga tashin hankali yayin da mayaka masu ikirarin jihadi suka soma kaddamar da hare-hare tun a watan mayun 2012.
Garuruwa da dama a arewa maso gabashin kasar sun zama kufai tun 2018, yayin da miliyoyin fara hula suka kauracewa gidajen su bayan mutuwar dubbai.
- Comments
- Facebook Comments