Akalla Falasdinawa 13 Da Suka Hada Da Kwamandojin Kungiyar Jihadin Musulunchi Guda Uku Aka Kashe A Zirin Gaza

0 168

Akalla Falasdinawa 13 da suka hada da kwamandojin kungiyar Jihadin Musulunchi guda uku aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza.

Wani jami’in kiwon lafiya na Falasdinu ya ce mata shida da yara hudu na daga cikin wadanda suka mutu kuma wasu mutane 20 sun jikkata.

Isra’ila ta ce ta kaddamar da farmaki kan ‘yan kungiyar Jihadin Musulunchi da ke barazana ga ‘yan kasarta.

Kungiyar Jihadin Musulunchi ta lashi takobin daukar fansa kuma ana sa ran mayakan za su mayar da martani da harba rokoki zuwa Isra’ila.

Masu aiko da rahotanni sun ce wani muhimmin al’amari shi ne yawan yadda kungiyar Hamas, mai iko da yankin, ta shiga fadan.

An rawaito cewa jami’an Isra’ila na shirye-shiryen shafe kwanaki ana gwabza fada.

Hare-haren dai su ne mafi muni a cikin kwanaki uku da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin Isra’ila da kungiyar Jihadin Musulunchi a watan Augustan da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: