Adadin kudaden babban banki kasa CBN take bin gwamnatin tarayya kawo yanzu ya kai kimanin naira Triliyan 15 da miliyan 51, wanda ya karu da sama da kaso 90 cikin dari idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 2 da biliyan 286 da ake bin gwamantin cikin shekaru 6 da suka gabata.
Bayaga haka wannan bashi bane kudin da ake bin gwamnatin tarayya kadai ba, ko a watan maris na wannan shekarar ma, an bayyana cewa anabin Nijeriya akalla naira Triliyan 33 da biliyan 11 kamar yanda hukumar bibiya da tattara basuka ta kasa ta bayyana.
Wadannan basussukan sunahda da wanda ake bin gwamantin tarayya da kuma na Jihohin kasar nan 36.
Kafin hakan dai a cikin watanni 6n farkon wannan shekarar, gwamnatin tarayya ta karbi bashin akalla naira Tiriliyan 2 da biliyan 4 daga CBN, sama da yanda ta karba a shekarar data gabata.
Kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki a watan Mayu na 2015 ana bin kasar nan kimanin naira Biliyan 648 da miliyan 26.