Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC da takwararta ta TUC a jiya sun yi watsi da hukuncin da kotun ma’aikata ta yanke wanda ya hana su tafiya yajin aiki farawa daga ranar Litinin.
Kungiyoyin na NLC da TUC sun sanar da haka bayan wata ganawa tsakanin gwamnatin tarayya da ma’aikata wanda aka tashi ba a cimma matsaya ba a jiya da yamma.
Biyo bayan karin farashin kudin wuta da na man fetur, gwamnati da kungiyoyin kwadago sun gana a ranar Talatar satin da ya gabata, a zaman an tashi baram-baram saboda kin amincewar gwamnati na janye karin kudaden, ko kuma bai wa ma’aikata tallafin rage radadin illar hakan.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Kungiyoyin na NLC da TUC daga nan suka ayyana tafiya yajin aiki da zanga-zanga wanda za a fara ranar Litinin mai zuwa. Dukkan kungiyoyin sunce zasu hada kai domin tabbatar da yajin aikin sosai.